Home » Wajen Da Basiru Dankiri Yake Tsare Shekaru 10 A Kano.

Wajen Da Basiru Dankiri Yake Tsare Shekaru 10 A Kano.

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Basiru Dankiri wani matashi ne mai shekaru 32 a duniya mazaunin garin Wailare dake karamar hukumar Makoda ta jihar Kano, wanda ake zargin yayansa mai suna Abdussalam Dandukulle, ya daure shi da sasari ( Sarka) tsawon shekaru 10 ba tare da bashi kyakkyawar kulawa ba.

Matashin dai an daure shi a cikin wani daki wanda babu kofar rufewa bare taga, kuma dakin ya kasance babu filasta  kuma ba a yiwa dakin dabe ba, Basirun yana kwanciya ne a cikin kasa ko tabarma babu, ya yi futu-futu da jikinsa babu kyan gani fuskarsa ta koma fiyot,  tamfar ta karamin yaro mai larular tamowa cikinsa ya koma  kurtsitsi, duk da cewa shekarun sa sun haura 30 amma idan ka kalleshi tamkar dan shekara 10 koma kasa da haka.

Basiru dai ya rasa kula da matallafa ta kowanne bangare , domin ba ya samun abincin kirki, babu ruwan sha balle na wannan kuma a wajen yake yin bayan gida da fitsari a wasu lokutan ma al’umma garin sun ce tsabar tsananin wahalar da yake ciki yakan ci bayan gidan nasa saboda yunwa.

Abdussalam Dandukulle shi ne yayan Basiru Dankiri, da ake zargin ya daure shi, ne saboda ya mutu ya mallake gonakin da ya gada bayan mahaifinsu ya rasu, duk da cewa ciki daya suka fito amma al’ummar yankin sun ce kwata-kwata baya tausayin dan uwannasa.

Sun kara da cewa kan wannan hali da yake ciki mutane da dama suna son yin Magana amma fa suna jin tsaron Dandukulle saboda ya ce duk wanda ya shigar masa gida don taimakawa Basiru za su yi shari’a da shi.

mahaifinsu ya rasu ya bar musu gonaki da dama wanda rahotanni suka tabbar da cewa akalla wanda Basiru Dankiri, ya samu gonaki guda biyar, kuma a wannan lokacin ne dagacin garin ya tashi tsaye don ganin an yiwa Basiru Magani har ya kira wasu yan uwansa suka yi shawarar a siyar da gonarsa don samun kudin maganin , wadanda suka yadda da shawarar, sai lokacin da suka zo daukrsa dan kaishi asibiti sun fuskanci matsala a gidan har aka hana su daukarsa.

ABDUSSALAM DANNDUKULLE,

Abdussalam Dandukulle

Abdussalam Dandukulle mazauni ne a garin Wailaren karamar hukumar Makoda ta jihar Kano, wanda yake gudanar da sana’ar sayar da Mangoro da Rake, wanda al’ummar yankin suka ce bada kowa yake yin shiri ba, duk da sana’ar da yake yi don yin mu’amula da kowa.

A bangarensa Dandukulle, ya ce bai daure dan uwansa domin ya cutar da shi ba, yayi hakan ne saboda matsalar shaye-shaye da yake kuma hakan ya jefa shi cikin wannan yanayi na rashin lafiya.

Wani abokin Basiru ya tabbatar da cewa baya yin shaye-shaye kamar yadda yayan nasa ya fada, amma a shekarun baya sun taba zuwa sun kamo maciji wanda suke ganin shi ne sillar shigar basiru cikin rashin lafiyar.

Sai dai ya kara da cewa akwai babban yayansu wanda Allah ya yi wa rasuwa shi ne yake da Basiru kafin ya rasu har ya samu lafiya, amma bayan rasuwarsa Dandukulle ya daure shi, ya daina bashi kulawa ta abinci da magani wanda hakan yana daga cikin abundaya kara jefa shi cikin rashin lafiyar domin ko Magana baya iya yi.

Dagacin Garin Wailare Alhaji Badamasi Halilu, ya bayyana cewa akwai alamu na rashin gaskiya a tattare da yayansa kasancewar an yi alkawari dashi za a kai shi asibiti a ranar Alhamis amma yayi tafiyarsa sannan wata tsohuwar mata ta dinga tada sababi cewa babu wanda zai dauki Basiru Dankiri ya kaishi asibiti.

Dagacin Wailare Ahaji Badamasi Halilu

Dagacin garin ya kara da cewa tuni ya sanarwa da baturen yan sandan Makoda don daukar mataki a hukumance saboda samun zaman lafiya.

Wanda ake zargin ya kuma shaida mana cewa shi iya bakin kokarinsa yake yi, kuma sun daure shi da gungumen itace ne bisa naman shawara da suka yi da wasu yan uwansu.

Yanzu haka dai al’ummar Wailare sun zura ido domin ganin matakin da hukumomin za su dauka don bincika wa tare da daukar mataki nag aba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?