Home » Cikin Hotuna: Yan Sandan Kano Sun Kama Masu Aikata Laifuka 78 Cikin Kwana 16.

Cikin Hotuna: Yan Sandan Kano Sun Kama Masu Aikata Laifuka 78 Cikin Kwana 16.

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Rundunar yan sandan jihar Kano ta cafke mutane 78 wadanda ake zargi da aikata laifukan, fashi da mamaki, dillancin mayagun kwayoyi, masu satar Shanu,yan Damfara, Barayi da kuma Yan Daba daga ranar 23 ga watan Afrilu zuwa 9 ga watan Mayu 2025.

Kwamishinan yan sandan jihar CP Ibrahim Adamu Bakori , ne ya bayyana hakan ga manema labarai, a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai a ranar juma’a.

CP Bakori, ya ce wannan nasara ta samu ne sakamakon samun bayanan sirri kan wadanda ake zargi, da aikata laifuka, inda suka kama wani shahararren mai dillancin miyagun kwayoyi , mai suna Sulaiman Danwawu mai shekaru 32 mazaunin Tudun Yola Kano.

Ya kara da cewa rundunar yan sandan ta taba kama Danwawu, a ranar 31 ga watan Yuli 2022, kuma an same shi da Katan 500 na kwayar Tramadol a wajensa, sannan suka gurfanar dashi a gaban kotu bisa zargin amma bayan ya fito ya ci gaba da aikata laifin

kwamishinan ya ce sun kama wani rikakken dan fashi da makami mai suna Mansur Sani, mazaunin karamar hukumar Rogo Kano,inda aka kwato bindigu kirar Beretta Pistol guda 2 da kuma harsasai 10.

Rundunar ta kama yan fashi da makami 5, masu dillancin kwayoyi 7, mai satar shanu 1, yan damfara 4, barayi 13 da kuma yan Daba 48.

Kayayyakin da kwato sun hada da bindigu kirar pistol 2 , harsasai 10, katon 4 na kwayar Pregabalin Tablets, Diazepam 63, Tramadol 47, katon 3 na Allurar Pentazocine, kwalaben kodin 25, sinki-sinki na tabar wiwi 5 da kuma kulli-kulli 65.

Sauran kayayyakin da aka samu nasarar kwatowa sun hada da matocin sata 8, adaidaita sahu 3, Babura 2, Adduna 12, Wukake 15, sai takaddun kudin na bogi dola guda 198 da kuma kudin Nijeriya naira dubu dari uku da dubu goma sha daya.

Ibrahim Adamu Ya kara da cewa an kwato wayoyin sata 12, Raguna 2, Tumaki 5, da Atamfofi da sauran kayayyaki.

A karshe kwamishinan yan sandan ya ce ba za su gajiya ba wajen yaki da aikata laifuka a jihar , inda ya tabbatar da cewa an samu raguwar aikata laifuka, kuma za su ci gaba sintiri a lungu da sako don fatattakar yan daba da masu ta’ammali da miyagun kwayoyi.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?