Jagoran jam’iyyar Economic Freedom Fighters wato EFF, ta Afirka ta Kudu wadda ita ce ta uku a girma a kasar, Julius Malema ya ce, zai taimaka wa Rasha da makamai saboda kasar tana yaki ne da tsarin mulkin mallaka na danniya.
A wata hira da ya yi da manemalabarai a Johannesburg, Mista Malema ya jaddada cewa Afirka ta Kudu Ƙawar Rasha ce kuma matsayin gwamnatin ANC na cewa ita Ƴar ba-ruwanmu ce ya shafi yakin Ukraine ne kawai.
Haka kuma jam’iyyar dan gwagwarmayar ta EFF na son ganin Afirka ta Kudu ta fice daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.
Kotun ta ICC ta bayar da umarnin kama shugaba Vladimir Putin a kan laifukan yaki amma kuma Malema ya yi alkawarin hana duk wani yunkuri na kama shi idan ya halarci taron kasashe biyar masu karfin tattalin arziki wato a mako mai zuwa a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu.