Wani Jirgin Sama Ya Saki Hanya A Legas

Wani jirgin saman United Nigeria Airlines ya zame, ya saki hanyarsa ta sauka da kimanin mita 200 a jiya Juma’a da daddare a babban filin jirgin saman Legas na Murtala Muhammad, al’amarin da ya firgita fasinjojin jirgin saman kamar yadda majiyoyi da dama suka sanar.

Wannan al’amari ya faru ne sanadiyar ruwan sama kamar da bakin ƙwarya inda ma’aikatan ceto da agajin gaggawa tare da ƴan kwana-kwana suka garzaya suka kai ɗauki kuma suka yi nasarar fitar da fasinjoji daga cikin jirgin saman.

Wata majiya daga babban filin jirgin saman na Legas ta ce abun ya faru ne a lokacin da jirgin saman yake sauka bayan dawowarsa daga Owerri, jahar Imo, kuma an auna arziki babu rahoton jin ciwo ko rasa rai.

Game da wannan al’amari da ya faru, har yanzu dai babu wani bayani ko ƙarin haske daga kamfanin jirgin saman da kuma hukumomin filin jirgin saman na Legas.

Post masu alaƙa

Da Fulani Aka Kama da Wuraren ƙera Makamai a Filato, da War Haka Duniya ta Dauka:-Zagazola Makama

Gwamna Bala Mohammed ya canja sheka daga jam’iyar PDP zuwa jam’iyyar APM

Gwamnatin Jihar Jigawa ta raba rancen naira miliyan dubu huɗu