CP Bakori ya buƙaci sabbin jami’an tsaron dazuka su nuna kware tare kaucewa cin hanci.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya buƙaci jami’an tsaron dazuka 1,002 da suka kammala horo su kasance masu ladabi da ƙwarewa wajen gudanar da aikinsu.

Kwamishinan ya yi wannan kira ne a bikin yaye jami’an da suka kammala horon watanni biyu a cibiyar horar da jami’an tsaro ta Corporate Security Institute da ke Zakirai, ƙaramar hukumar Gabasawa.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce CP Bakori ya buƙaci jami’an su mutunta haƙƙin bil’adama, guji cin hanci da rashawa da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, tare da haɗa kai da sauran hukumomin tsaro.

Ya kuma jaddada cewa jami’an ba za su yi aiki su kaɗai ba, domin suna daga cikin tsarin haɗin gwiwar tsaro da ya ƙunshi ’yan sanda, DSS da sojoji.

Kwamishinan ya tabbatar musu da goyon bayan hukumomin tsaro wajen kare dazuzzuka, al’ummomin yankunan kan iyaka da dukiyoyinsu.

Post masu alaƙa

Kwankwaso ya zargi Abba da amfani da EFCC don ɓata masa suna

Yan kasuwar kano sun ƙuduri aniyar haɗa gwiwa da ’yan sanda wajen yaƙi da shan ƙwayoyi, ’yan daba da sata

Rundunar yan jihar Kano ta kama mutane 3 da zargin fashi da makami da garkuwa da cin zarafin mace a Rogo.