Wani jirgin saman kamfanin United Nigeria Airlines ya zame, ya saki hanyarsa ta sauka da kimanin mita 200 a babban filin jirgin saman Legas na Murtala Muhammad ranar Juma’a da daddare, al’amarin da ya firgita fasinjojin jirgin saman kamar yadda majiyoyi da dama suka sanar.
Wannan al’amari ya faru ne sanadiyar ruwan sama kamar da bakin ƙwarya inda ma’aikatan ceto da agajin gaggawa tare da ƴan kwana-kwana suka garzaya suka kai ɗauki kuma suka yi nasarar fitar da fasinjoji daga cikin jirgin saman.
Wata majiya daga babban filin jirgin saman na Legas ta ce abun ya faru ne a lokacin da jirgin saman yake sauka bayan dawowarsa daga Owerri, jahar Imo, kuma an auna arziki babu rahoton jin ciwo ko rasa rai.
Sai dai game da wannan al’amari da ya faru, babu wani bayani ko ƙarin haske daga kamfanin jirgin saman da kuma hukumomin filin jirgin saman na Legas, har zuwa lokacin da aka fitar da labarin.