Rundunar yan sandan jahar Kano ta haramta gudanar da hawan Kilisa, da na angwanci da kuma zaman majalisi har sai an nemi izini daga Fadar Sarkin Kano.
Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanya wa hannu.
CP Gumel ya ce sun ɗauki wannan mataki ne sakamakon yadda wasu matasa ke yunƙurin mayar da hannun agogo baya kan abinda ya shafi tsaro a jahar domin sun gano cewa a irin wuraren ake aikata laifuka.