Rundunar yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa bikin Takutaha na 2026, wanda aka gudanar a ranar 1 ga Satumba, ya gudana cikin kwanciyar hankali a sassan jihar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar Kano bisa haɗin kai da bin doka da oda da suka nuna yayin bikin.
Rundunar ta ce, a yayin aiyukan tsaro da aka gudanar kafin da kuma bayan bikin, an kama mutane 79 bisa zargin aikata laifuka daban-daban.
Haka kuma, jami’an tsaro sun kwato makamai masu haɗari da miyagun ƙwayoyi.
Jami’in Hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan waɗanda aka kama, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala binciken.
