Hukumar gasar zakarun nahiyar Turai UEFA za ta biya kudin tikitin magoya bayan Liverpool, wadanda suka tsaya don kallon wasan karshe na Champions League a Paris dake ƙasar Faransa.
Hakan ya biyo bayan wani kwamiti mai zaman kansa da ya binciko cewar UEFA ce ta haddasa turmutsitsin da ya faru, kafin wasan karshe tsakanin Liverpool da Real Madrid.
Ga Wani Labarin: Wani Jami’in Sojan Ƙasar Nan Ya Harbe Abokan Aikinsa Har Lahira
Magoya baya da dama ba su samu damar shiga kallon wasan ba, an kuma harba barkonon tsohuwa a fafatawar da aka yi lattin minti 36 kan fara wasan.
UEFA ta ce za ta biya dukkan tikiti 19,618 da aka bai wa magoya bayan liverpool, domin kallon fafatawar da aka yi a Faransa.
Real za ta karbi bakuncin Liverpool a wasa na biyu ranar 15 ga watan Maris a fili wasa na Santiago Bernabeu.
Liverpool, za ta je Sifaniya da kwarin gwiwa, bayan da ta doke Manchester United 7-0 ranar Lahadi a Premier League a Anfirld.
Ita kuwa Real Madrid, wadda Barcelona ta ba ta tazarar maki tara a teburin La Liga, ta je ta tashi 0-0 da Real Betis ranar Lahadi.