Daga Mujahid Wada Musa
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gurfanar da wasu matasa hudu a gaban kotun majistiri mai lamba 43, dake zaman ta a unguwar Gyadi-gyadi, karkashin jagorancin mai shari’a Kabiru Sallau, bisa zarginsu da aikata laifuka hudu.
Wadanda ake zargin sun hada da, Haruna Abdullahi, Hamisu Lawan, Ibrahim Zubairu da kuma Musa Isma’il, ana tuhumarsu da laifukan hada kai da samar da rauni da shiga kungiyar batagari da kuma aikata fashi da makami.
Tunda fari ana zargin matasan sunje unguwar Medile dake karamar hukumar Kumbotso ta jihar, suka haura gidajen jama’a tare da kwace mu su kudade da sauran kayan amfani yau da kullum.
Lauyar gwamnatin jihar Kano Barista Safiya Yahya Yalwati, ta karanto mu su kunshin tuhume-tuhumen da ake yi mu su, amma dukkan wadanda ake tuhumar sun musanta zargin.
Alkalin kotun ya ɗage ci gaba da sauraran shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Janairun 2025, tare da bayar da umarnin a tsare su a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya.