Home » Rukuni na 3 na ma’aikatan Muhasa TVR sun sake samun horaswa a fannin Talabijin

Rukuni na 3 na ma’aikatan Muhasa TVR sun sake samun horaswa a fannin Talabijin

by Anas Dansalma
0 comment
Rukuni na 3 na ma'aikatan Muhasa TVR sun sake samun horaswa a fannin Talabijin

Hukumar Gidan Radio da Talabijin na Muhasa ta kara kaimi wajen soma gabatar da shirye-shiryenta na talabijin wanda a yanzu haka aka fara gwaji akan dikodar Startimes a lamba 170.


A cigaba da wannan ƙoƙari, hukumar ta sake tura wasu ma’aikatan rukuni na uku domin samun horaswa don sanin makaman aiki.

A ranar Juma’ar da ta gabata 21 ga watan Yulin shekarar da muke ciki ne ma’aikatan Muhasa rukunin na uku, suka fara karɓar horaswa ta musamman daga kanfanin Moving Image a kan fannin talabijin.

A yayin haraswar, an taɓa ɓangarori da dama da suka hada da fara sanin dokoki da ƙa’idojin aikin jarida da aikin jarida aikace ta fuskar tsarawa da gabatar da shirye-shirye da sauransu.

Rukuni na 3 na ma'aikatan Muhasa TVR sun sake samun horaswa a fannin Talabijin

A yayin da yake gabatar da jawabin kammalawa, manajan darakta na kanfanin Moving Image ya godewa gidan Talabijin da rediyo na muhasa bisa amincewa da kanfanin domin ba wa ma’aikatanta horo.

Ita kuwa mataimakiyar shugaban wannan gida, Hajiya Aishatu Sule ta ja hankalin wadanda suka samu horon ne kan su yi amfani da abin da suka koya wajen inganta ayyukansu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi