Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta bakin kakakin rundunar DSP Haruna Kiyawa, ya bayyana yadda rundunar ta yi nasarar kama wasu mutane bakwai daga cikin gungun ‘yan daba 2 da ke zargi da fadan daba a daidai kasuwar Rimi da cikin kwaryar birnin Kano.
Tuni dai kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano ya ba da umarnin dawo da waɗanda aka kama sashen binciken manyan laifuka da ke Bompai domin fadada bincike.
Sannan ya bayyana mana yadda wani jami’in rundunar ya samu raunuka wanda tuni aka mika shi zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.