Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin sababbin shuwagabannin hukumomin KAROTA, REMASAB da REDIYON KANO da kuma wasu da za su shiga cikin masu bada shawarwari na musamman a gwamantinsa.
Mai taimakawa Gwamnan jihar Kano a kafofin sadarwa na zamani, Salisu Yahaya Hotoro ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook.
Sanarwar ta bayyana cewa an naɗa honorable Hisham Habib a matsayin sabon daraktan gudanarwar radio Kano wanda a baya ya kasance jami’in hulɗa da jama’a a ma’aikatar shari’a ta jiha, kuma ya yi aiki a kafafen yaɗa labari daban-daban a ƙasar nan.
An kuma naɗa Engr. Faisal Mahmud Kunbotso a matsayi shugaban hukumar kula da ababen hawa ta jiha wato KAROTA.
Sauran da aka nada sun hada da Injiniya Sulaiman Sani a matsayin mai ba wa gwamna shawara na musamman kan harkar noman rani da madatsan ruwa.
Sai Abdullahi Shu’aibu a matsayin mashawarci na musamman kan Ma’aikatar Fansho, da malam Yusuf Imam Shuaibu a matsayin mashawarci na musamman kan harkokin matasa da wasanni.
Haka kuma an naɗa Sadiya Abdu Bichi a matsayin mashawarciya ta musamman ga gwamnan Kano kan Mata da kuma masu bukata ta musamman.