Wasu matasa a unguwar Dorayi dake jihar Kano sun bankawa wani da ake zargin barawon waya ne wuta, bayan da kwace wayar wata mata.
Rahotanni sun ce barawon ya chakawa matar wuka a kirjin ta kafin matasan su hallaka shi ta hanyar kone shi da taya.
Tuni aka garzaya da matar zuwa asibiti cikin mummunan yanayi domin samun kulawar gaggawa daga likitoci, ya yin da jami’an tsaro suka iso wurin suka dauki konanniyar gawar barawon, don gudanar da bincike.
Har zuwa wannan lokaci rundunar yan sandan jihar Kano, bata fitar da wata sanarwa ba kan faruwar lamarin.

