Rahotanni daga jihar Nassarawa na nuni da yadda wata mata mai juna biyu ta rasa ranta saboda rashin likitan da zai duba ta a asibiti.
Wannan al’amari ya faru bayan fara wani yajin aiki na kwanaki biyar da likitoci masu neman kwarewa kuma da ke aiki da asibitin gwamnatin jihar suka tsunduma.
An shirya yi matar da wannan al’amari ya faru da ita ne aiki a wani asibitin kwararru mai suna Dalhatu Specialist, sai dai wannan aiki bai samu ba saboda yajin aikin da likitocin suka fara wanda aka bar matar kwance tana jiran aiki har rai yai halinsa.
Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa tuni aka fara kwashe marasa lafiya da neman taimakon gaggawa zuwa wasu asibitocin kudi da ma kai su zuwa wasu jihohi masu makwabtaka da jihar ta Nassarawa.
Ana sa ran dai za a kammmala wannan yajin aikin ne a ranar 10 ga watan da muke ciki wanda ya shafi manyan asibitoci 19 da ya hada har da asibitin Dalhatu Araf wanda mallakin gwamnatin jihar ne.
A ɓangaren mijin matar da ta rasa ranta mai suna Abubakar Liman ya ce ya ɗauki faruwar wannan al’amari a matsayin kaddara, sai dai yana mai rokon gwamnatin jihar da ta taimaka ta biya waɗannan likitoci buƙatunsu domin kauce wa faruwar makamancin wannan mummunan al’amari.