Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta zayyana jihohi 14 da yankuna 31 da ka iya fuskantar mamakon ruwan sama mai karfin gaske wanda zai iya haifar da ambaliyar ruwa daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Yuli.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mista Ibrahim Farinloye, Kodinetan NEMA, ya fitar.
Farinloye ya bukaci masu ruwa da tsaki a jihohin da abin ya shafa da su dauki matakan kariya domin dakile asarar rayuka da dukiyoyi.
Jihohin da yankunan da abin ka iya shafa su ne kamar haka:
Filato: Langtang da Shendam
Kano: Sumaila da Tudun Wada
Sakkwato: Shagari, Goronyo da Silame
Delta: a garin Okwe
Kaduna: a garin Kachia
Akwa Ibom: a Upenekang
Adamawa: a garuruwan Mubi, Demsa, Song, Mayo-belwa, Jimeta da Yola
Katsina: birnin Katsina, Jibia, Kaita da Bindawa
Kebbi: Wara, Yelwa da Gwandu
Zamfara: Shinkafi da Gummi
Borno: Briyel
Jigawa: Gwaram
Kwara: Jebba
Neja: Mashegu da Kontagora
Farinloye ya gode wa Hukumar Hasashen Ruwan Sama (FEWS) da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya Abuja bisa bayar da bayanan daminar bana a kan lokaci.