Kamfanin Meta wanda shi ne mamallakin Facebook da Instagram, ya kaddamar da manhajar sabon shafin sada zumunta da muhawara, mai suna ‘Threads’ a matsayin kishiya ga Twitter.
Shafin na Threads, yana dauke da abubuwa kamar yadda Twitter yake da su kuma wanda yake da shafin Instagram zai iya samunsa ta wannan shafin cikin sauki.
Bayan ‘yan sa’o’i da kaddamar da sabon shafin, an samu sama da mutum miliyan 10 da suka yi rajista a cewar shugaban kanfanin na Meta.
Shahararrun mutane kamar Jennifer Lopez da Shakira da Hugh Jackman tuni suka bude nasu sabon shafin na Thread.
Su ma wasu daga cikin kanfanonin jarida kamar The Washington Post da Economist tun suka yi hanzarin bude shafinsu a kan wannan sabon dandali.
Wata mai sharhi kan al’amuran sada zumunta, Jasmine Engberg, na ganin an samu wannan shafi ne sakamakon irin riƙon sakainar kashi da kuma sabbin tsare-tsare da mamallakin kanfanin Twitter, Elon Musk, ke yi wa shafinsa nasa wanda hakan ya sa takwaransa Zuckerberg yin amfani da damarsa.
Tana ganin akwai yuwuwar shafin na Thread ya samu karbuwa la’akari da mabiya da Instagram ke da shi da kuma inganta fasahar Thread da aka yi.