A cigaba da bikin cika shekaru 60 da kafa hukumar a nan Kano, tsohon shugaban hukumar Muhammad Babandede ya yi kira ga gwamnatin Kano da ta samar da wata kasuwa da za ta rika ci ba dare ba rana domin inganta kasuwanci a jahar dama kasa bakiɗaya.
Ya yi wannan kira ne lokacin da yake gabatar da mukala a wajen taron, inda ya ce kasuwanci zai taimaka wajen magance matsalar daba a jihar.