580
Tsohon Shugaban Hukumar Shigi da Fici ta Kasa, Muhammad Babandede, shugaba na 16 kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Muhasa ciki har da Muhasa TVR, na daya daga cikin wadanda Hukumar ta karrama a shekaran jiya a Abuja a lokacin da aka yi bikin cika shekaru sittin da kafa hukumar.
An karrama Muhammad Babandede da lambar yabo mai daraja, wadda Shugabar Riko ta Hukumar, Caroline Wura-Ola Adepoju ta miƙa masa.