Masu ƙwacen waya sun kashe wani ma’aikacin Jami’ar Northwest da ke Kano, Buhari Imam, ta hanyar daɓa masa wuƙa a ciki.
Rahotanni sun bayyana cewa ɓarayin sun ritsa shi ne a yankin unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso, inda suka sossoke shi da wuka a ciki kuma suka kwace wayarsa, a ranar Laraba.
Kafar yaɗa labarai ta BBC ta ruwaito cewa malamin ya rasu bayan da aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, a ranar Juma’a.
- Gobe Za A Rufe Kasuwar Singa Domin Yashe Magudanan Ruwa
- Najeriya Ta Buƙaci MDD Ta Kawo Ƙarshen Yaƙi Tsakanin Iran Da Isra’ila
Kwamared Bashir Muhammad Shugaban ƙungiyar ma’aikatan jami’ar (NASU), wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya buƙaci gwamnatin Jihar Kano da sauran hukumomi da su ɗauki tsattsauran mataki a kan kisan.