Daga Suraj Na Iya Idris Kududdufawa
Sakamakon mamakon ruwan sama da ake ci gaba da tafkawa a sassa daban-daban na duniya, a yankin kasar Nijar an yi wani gagarumin ruwan sama a jihar Maradi inda yayi asarar rayuka da dama.
Biyo bayan ruwan da aka sheka a ranar Juma’a ya ruguza gidaje da dama hakan yayi sanadiyyar rasa rayuka.
A binciken da aka gudanar dai zuwa yanzu a kalla mutane 50 sun rasa rayukansu sannan kuma sama da mutane 100 sun jikkata.
Muhasa Radio ta tattauna da daya daga cikin mazauna ganin na Maradi mai suna Rabiu ta wayar tarho inda ya bayyana cewar mafiya yawan gidajen da ruwa ya cinye irin tsofaffin gidaje ne da su kai shekaru 60 zuww 70 da ginawa.
“Ruwa ya yi mana barna sosai kuma ya kashemin ‘yan uwa na, domin an kwashe awanni ana ruwa sosai” acewar Rabiu.
Daga karshe an bayar da shawarar cewa ya kamata a dinga fitar da magudanan ruwa tun kafin lokacin zubar ruwan sama yayi.