Home » Yan Arewa Su Koyi  Dabarun Kare Kai- ACF

Yan Arewa Su Koyi  Dabarun Kare Kai- ACF

by Mubarak Ibrahim Mandawari
0 comment

Ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa(ACF) ta yi kira kan yadda za’a wayar da kan mutanen Arewacin Najeriya, game da muhimmancin kare kansu, duba da yadda matsalar tsaro tayi ƙamari a yankin.

Da yake gabatar da jawabi a taron kwamitin zartarwar ƙungiyar na ƙasa, ACF Mamman Mike Osuman ( SAN), ya nuna takaici kan yadda hare-hare da satar mutane da kisan gilla suka addabi Jihohin Arewacin ƙasar.

“Muna fama da matsalolin yan bindiga da ta’addanci da kuma masu satar mutane,” a cewar Osuman.

Akwai buƙatar mu ilmantar da al’ummar mu kan muhimmancin kare kansu don yaƙar waɗannan matsaloli.

Osuman ya kuma yi gargaɗi da cewa matsalar tsaro bata tsaya a iya Arewacin Najeriya ba, matsala ce da ta shafi ƙasa baki ɗaya, wanda take buƙatar ɗaukar matakin gaggawa

Ya zama dole Gwamnoni da yan majalisu da kuma sarakunan gargajiya su haɗa kai don magance waɗannan matsaloli.

Shugaban ya kuma jinjinawa ƙungiyar League of Northern Democrats, ƙarƙashin jagorancin Dokta Umar Ardo da wasu manyan Arewa, wanda ya bayyana manufofin su sun yi daidai da na ACF

Sai dai ya jaddada cewa lokaci ya yi da za’a mayar da hankali kan ɗaukar matakan gaggawa maimakon jiran mafita ta siyasa.

“Dole ne mu mayar da hankali kan bunƙasa tattalin arziƙi, ilimi, gine-gine, da tabbatar da tsaro domin sake gina Arewa,” in ji Osuman.

Matsalar rashin tsaro na ƙara yin ƙamari a yankin Arewa, wanda hakan yake kawo nakasu a harkokin kasuwanci da aikin gona da ilimi da sauransu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?