Yan Bindiga Sun Saki Birgediya Janar Tsiga

Birgediya Janar Maharazu Tsiga Mai ritaya ya kuɓuta bayan shafe kwana 56 a hannun ’yan bindiga.

An sace Janar Tsiga, wanda Tsohon shugaban Hukumar NYSC ne, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025.

Hakazalika, aharan sun sace mutum tara a tare da shi a lokacin da suka kai harin.

Duk da cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa, ’yan bindigar sun ci gaba da tsare shi na tsawon makonni.

Wani daga cikin iyalansa ya bayyana cewa bayan maharan sun karɓi kuɗin, sai suka yi shiru har na tsawon mako guda, kafin daga bisani su kira iyalansa a ranar 11 ga watan Maris, inda suka ba shi ya yi magana da su.

Daga baya, sun sake neman ƙarin kuɗi, amma iyalan nasa ba su ƙara musu ba.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa yanzu haka yana Jihar Zamfara, wanda daga nan za a kai shi Abuja.

Wani jami’in soja ya tabbatar da sakinsa, inda ya ce yana cikin ƙoshin lafiya.

Post masu alaƙa

NSCDC ta rufe wani gida da ake zargin ana safarar jarirai a Legos.

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta kama wanda ake zargi da safarar Alburusai a tankin Babur

‘Iran ta buɗe wa wani jirgi wuta a mashigar Hormuz