Aƙalla mutum biyar ne suka rasu lokacin da ’yan bindiga suka kai hari wani Masallaci, yayin da ake tsaka da sallar Asuba a garin Yandoto da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.
Shaidu sun ce maharan sun kutsa cikin Masallacin inda suka fara harbi ba tare da ƙaƙƙautawa ba, inda suka kashe mutum biyar nan take tare da jikkata wasu da dama.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun kuma yi awon gaba da wasu Masallata.
Ya bayyana lamarin a matsayin “rashin imani da ta’addanci.”
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda suka ji rauni yanzu haka suna asibiti ana kula da su.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya ce ba shi da labarin faruwar lamarin.
Harin na zuwa ne mako guda bayan makamancin irinsa a ƙauyen Gidan Turbe, wanda shi ma ke Ƙaramar Hukumar Tsafe, inda aka yi garkuwa da aƙalla Masallata 40 yayin da suke tsaka da sallar asuba.
- Kungiyar Likitocin Nijeriya Ce Zata Tantance Sahihancin Rashin Lafiyar Nnamdi Kadu: Kotu
- Kungiyar Likitocin Nijeriya Ce Zata Tantance Sahihancin Rashin Lafiyar Nnamdi Kadu: Kotu
A wani labarin kuwa, masu haƙar ma’adinai 100 ta ɓarauniyar hanya ake fargabar sun rasu bayan rami ya rufta musu a kauyen Kadauri da ke Ƙaramar Hukumar Maru, a jihar Zamfara.
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya auku a ranar Alhamis, inda ramin ya rufe mutane da dama.
Kafin ceto waɗanda suka maƙale, rai ya yi halinsa, sakamakon ɗaukar lokaci da suka yi a ƙarƙashin ƙasa.
A halin yanzu, an tono gawarwakin mutum takwas; dukkaninsu mazauna ƙauyen Mekwanugga.
An kai garinsu domin yi musu jana’iza, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
