• Home  
  • Zamfara: ‘Yan bindiga sun sace daliban da ba san adadinsu ba
- Labarai

Zamfara: ‘Yan bindiga sun sace daliban da ba san adadinsu ba

Rahotanni  daga jihar Zamfara na cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari gidajen kwanan ɗaliban Jami’ar dake Gusau, tare da sace ɗaliban da  har yanzu ba a tantance adadinsu ba.

zamfara

Rahotanni  daga jihar Zamfara na cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari gidajen kwanan ɗaliban Jami’ar dake Gusau, tare da sace ɗaliban da  har yanzu ba a tantance adadinsu ba.

Lamarin dai ya faru ne da asubahin Juma’ar nan, inda rahotanni ke cewa maharan sun kutsa gidajen kwanan ɗalibai uku a unguwar Sabon Gida da ke maƙwaftaka da jami’ar.

Bayanan na cewa ƴan bindigar sun samu nasarar kwashe kusan dukkanin ɗaliban da ke zaune a gidajen da ke daura da jami’ar.

Har yanzu dai hukumomi ba su yi ƙarin bayani kan lamarin ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai