Yan Bindiga Sun Sace Mata 5 A Kano

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari garin Ƴankwaɗa da ke Karamar Hukumar Shanono ta Jihar Kano, inda suka yi awon gaba da mata shida ciki har da masu shayarwa, tare da harbin mutum ɗaya.

Wannan na zuwa ne mako guda bayan kai irin wannan harin a wasu kauyuka a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa, da suka yi iyaka da Jihar Katsina wadda da taɗe tana fama da hare-haren ‘yan bindiga.

Wani mazaunin yankin da abin da ya faru da ya zanta da BBC ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce maharan sun isa garin ne da misalin ƙarfe na 10:30 zuwa 11 na dare.

“Wannan karon sun canja salo ne, inda suka shigo a ƙafa maimakon a babura da suka zaba zuwa domin su ɓatar da kama. Sai da suka shiga tsakiyar gari sai suka buɗe wuta. Da mutane suka watse, sai suka shiga gida-gida suka kwashe mata guda shida ciki har da masu shayarwa, sannan suka harbi wani mutum ɗaya a gidansa.”

Sai dai ya ƙara da cewa daga cikin matan da aka kwasa, guda biyu sun koma, “amma sun tafi da guda huɗu daga cikinsu. Sannan wanda aka harba yana jinya.”

BBC ta yi yunƙurin jin ta bakin kakakin rundunar ƴansanda na jihar Kano, amma haƙarta bai cimma ruwa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *