Yan Boko Haram Da ISWAP 200 Sun Mutu Sakamakon Rikici A Tsakaninsu

Rahotanni na cewa rayukan mayaƙa 200 sun salwanta a sanadiyyar wani rikicin cikin gida tsakanin ’yan ƙungiyar Boko Haram da na ISWAP a Jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Nijeriya.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa rikicin ya ɓarke ne a yankin Dogon Chiku, kusa da Tafkin Chadi, a ranar Lahadi.

Bayanai sun ce wannan dai na daga cikin rigingimun da suka fi zafi tun bayan da ɓangarorin suka yi hannun riga saboda saɓanin ra’ayi a shekarar 2016.

Wani ɗan sa-kai da ke taimaka wa dakarun Nijeriya wajen sa ido kan lamurran tsaro, Babakura Kolo, ya ce sun ƙirga gawarwakin aƙalla mayaƙa 200.

“Mun ƙirga aƙalla gawarwaki 200, mafi yawansu na bangaren ISWAP,” in ji shi.

Shi ma wani tubabben ɗan Boko Haram mai suna Saddiku, wanda ke bin diddigin lamurran ƙungiyoyin, ya tabbatar da faruwar rikicin.

A cewarsa, “an kashe aƙalla ’yan ISWAP 200, kuma an ƙwace makamai da dama. Sai dai daga ɓangaren Boko Haram an rasa mayaƙa huɗu kacal.”

Majiyoyin tsaro ma sun tabbatar da aukuwar rikicin, inda cikin farin ciki wata majiyar sirri ta ce, “muna da bayanan da suka nuna an kashe mayaƙa fiye da 150, kuma wannan abu ne da ke rage musu ƙarfi.”

Tun bayan rabuwa tsakanin Boko Haram da ISWAP a shekara ta 2016, ɓangarorin biyu sun riƙa kai wa juna farmaki lokaci zuwa lokaci, musamman a yankin Tafkin Chadi da wasu sassan Jihar Borno.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *