Wasu ’yan bindiga sun sako mata da kananan yara 45 da ke hannunsu a yankin Karamar Hukumar Bakori da ke Jihar Katsina.
A ranar Litinin ne ’yan bindigar karkashin jagoranci wani dan ta’adda mai suna Isiya Kwashen Garwa suka sako mutanen a yayin wani taron sulhu.
Wakilin Karamar Hukumar Bakori a Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Injiniya Abdurrahman Kandarawa ya halarci taron mika mutanen, wanda aka shirya domin shaida cewa ’yan bindigar sun rungumi zaman lafiya a karamar hukumar.
- Gwamnan Taraba Ya Dakatar Da ficewa Daga PDP Saboda Sace Dalibai A Kebbi
- Hotunan Yadda Fada Ya Barke A Hedikwatar Jam’iyyar PDP

Dan majalisar ya bayyana jin dadi bisa yadda ’yan bindigar suka cika alkawarin sulhu da zaman lafiyar da aka yi da su a karamar hukumar.
A nasa jawabin, Isiya Kwashen Garwa ya yi kira ga dukkan bangarorin da suka cika alkawarin da suka dauka domin samun zaman lafiya mai dorewa.
Ya kuma yi kira da a bar ’yan bindigar da aka yi sulhu da su, su rika shiga cikin al’umma ba tare da wata tsangwama ba.

