Home » ‘Yan Jarida Sun Sami Horo

‘Yan Jarida Sun Sami Horo

by Hassan Abdu Mai Bulawus
0 comment

Gidauniyar MacAurthar tare da haɗin gwiwa da Jaridar Stallion Times sun horar da ‘yan jarida dabarun shirya rahoton bin ƙwaƙƙwafi wato (investigative report) da kuma yadda za a yaɗa rahotannin zuwa kafafen sadarwa mabambanta.

An gudanar da taron ne a Cibiyar ‘Yan jarida ta NUJ da ke unguwar Farm Centre a cikin birnin Kano.Manyan da ƙananan ‘yan jarida daga kafafan sadarwa daban-daban ne suka halarci taron ciki har da ma’aikatan Muhasa TV & Radio, Hassan Abdu Mai Bulawus da Fatima Muhammad Adam.

Farfesa Mai Nasara Yakubu Kurfi, Shugaba Sashen Aikin Jarida na Jami’ar Bayero da ke Kano, wanda shi ya gabatar da maƙala a yayin horarwar, ya ce, rahoton bin diddigi na taimaka wa al’umma wajen sanin abin da ake ɓoye musu na rashin gaskiya.

Shi ma Kwamared Abbas Ibrahim Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida Reshen Jihar Kano, ya ce horon na da muhimmancin ga ‘yan jarida sosai.

Kuma ya hori waɗanda suka sami horon da su tabbatar sun yi amfani da abin da suka koya.Malam Isyaku Ahmad shi ne Jaridar Stallion Times, kuma su suka shirya taron ya ce suna gabatar da irin taron ne a-kai-a-kai, amma wannan shi ne na ƙarshe a wannan shekarar.

Daga ƙarshe shi ma ya buƙaci mahalarta horarwar da su ci gaba aiwatar da abin da suka koya.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?