Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da biyan wani ɓangare na albashin mambobin Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) wanda aka riƙe sakammakon dokar Ba-aiki-ba-biya wadda aka saka musu biyo bayan yajin aikin da suka kwashe watanni takwas suna yi.
An fara yajin aikin tun daga ranar 14 ga watan Fabarairu, 2022 zuwa 17 ga watan Oktoba, 2022.
Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara a Kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Juma’a.
Nglale ya ce Shugaba Tinubu ya yi hakan ne bisa damar da doka ta ba shi ta tausayawa wato “the Principle of the Presidential Prerogative of Mercy”.
