Tawagar ’yan jarida kimanin su 14 da suka fito daga kafafen yaɗa labarai dabam-dabam suka gamu da mummunar hatsarin mota a yayin da suke cikin tawagar Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC).
Tawagar da suke tafiya a ƙarƙashin jagorancin ƙaramin Ministan Raya Yankuna, Alhaji Uba Maigari Ahmadu a yayin da suke ziyarar buɗewa da miƙa ayyukan da hukumar NEDC ta gudanar a jihar Bauchi zuwa hannun gwamnatin jihar.
Hatsarin ya faru ne a kan titin Yashi zuwa Yelwan Duguri da ke cikin ƙaramar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi yau ranar Jumma’a, bayan Ministan ya ƙaddamar da katafaren makaranta a garin Yalwan Duguri.
yan jaridun sun samu munanan raunuka raunuka daban-daban yayin da ake ƙoƙarin samar musu da agajin gaggawa a asibitin Yelwan Duguri daga bisani kuma za a wuce da su babban asibiti a Bauchi domin neman musu kulawar likitoci.
‘Yan jaridun da abin ya shafa waɗanda suka fito daga gidajen talabijin na Channels, AIT, NTA, BAT Arise da wasu irin su wakilan manyan jaridun na Guardian, the Nation, Kanfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) da sauran su da dama.
- Majalisar ƙoli kan shari’ar musulunci ta nanata buƙatar a cire shugaban INEC
- Gwamna Namadi ya jagoranci babban taron fasaha a Argentina domin bunƙasa noman alfalfa da ci gaban kiwo a Jigawa
Hatsarin ya faru ne jim kaɗan bayan da tawagar suka buɗe aikin makarantar GSS a Yelwan Duguri, inda suke kan hanyarsu ta zuwa domin buɗe wasu ayyukan.
Daga cikin waɗanda suke cikin tawagar har da Minista, shugabannin NEDC, Shugaban Hukumar da Darakta Manaja, da Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi da sauransu.
Kazalika, Wakilin Dailytrust, wanda ke cikin tawagar ya shaida cewa, motar da ta gamu da hatsarin ɗaya ce daga cikin motocin da ‘yan jaridan ke amfani da su a yayin aikin ɗauko labarin. Ya kuma tabbatar mana da cewa kayayyakin aikin jarida dama kamar su Kyamarori sun lalace. Amma babu asarar rai.

