Batun taliyar Indomie ya jefa ‘yan Nijeriya da dama cikin rudani duba da yadda suka shafe tsawon shekaru suna durawa cikinsu wannan taliyar, musamman yara kanana da wadanda suke yawan ziyartar wuraren masu sayar da shayi, Sai dai duk da hakan, masana na nuni da cewa al’ummar Nijeriya na cin taliyar ‘yan yara fiye da tunani.
hukumar kula da ingancin kayayyakin abinci da magunguna a Nijeriya (NAFDAC), ta fito ta shelanta na haramta shigowa da amfani da taliyar da ake shigowa da ita cikin Nijeriya bisa zargin tana haifar da cutar kansa ga masu amfani da ita.
Da take magana kan wannan matakin, Darakta Janar ta hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta shaida cewar hukumar za ta fara gudanar da gwaje-gwaje kan samfurin wanda ake shigo da ita daga waje domin kara gano hakikanin gaskiyar lamarin.