Yan sanda sun kama mutum 4, sun ƙwato dabbobi sama da 300 a Gombe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama mutum huɗu da ake zargi da satar dabbobi, tare da ƙwato dabbobi sama da 300 a wani samame da suka kai a sassa daban-daban na jihar.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama mutanen ne a ranar 8 ga watan Janairu, 2026.

An kama su ne a ƙananan hukumomin Yamaltu-Deba, Kaltungo da Balanga, biyo bayan haɗin gwiwar ’yan sanda, jami’an ’yan sa-kai da kuma mafarauta.

Ya bayyana cewa a Jagali ta Yamma, an kama wani matashi mai shekara 17 ɗauke da awaki 49, inda aka gano 16 daga cikinsu mallakar wani mutum da aka sace masa.

Haka kuma, a Kaltungo, an kama wani yaro mai shekara 16 ɗauke da tumaki 115 da jaki guda ɗaya, inda aka gano 23 daga cikin tumakin na wasu mutane ne.

A wani samame kuma, jami’an tsaro sun kama wani matashi mai shekara 22 a Kasuwar Dabbobi ta Gombe ɗauke da shanu biyu da ake zargin na sata ne.

Hakazalika, an kama wani mutum ɗauke da tumaki 159 da awaki biyar, inda aka gano 30 daga cikinsu mallakar wani mutum ne.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, Umar Ahmed Chuso, ya yaba da haɗin gwiwar jami’an tsaron.

Ya ce rundunar za ta ci gaba da bincike tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban kotu.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *