A wani ci gaba, Jaridar Dailytrust ta wallafa a shafinta cewa an kame mata wani ma’ikacinta, Ben Uwalaka, da ke bakin aiki a lokacin da yake ɗaukar hotunan yadda zanga-zangar ma’aikatan sufurin jirgin sama ke wakana a garin Ikko.
Wannan al’amari ya faru ne a filin sauka da tashin jirage na Murtala Muhammed, inda jami’an suka kama shi tare da lalata masa kyamarar da yake aiki da ita.
A yayin haɗa wannan rahoto, ɗan jaridar ya shafe kusan sama da awa ɗaya yana tsare a ofishi yan sandan da ke a cikin filin sauka da tashin jiragen.
Wannan na zuwa ne dai a lokacin da ƙungiyoyin ma’ikatan Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasa ke Gudanar da yajin aikin jan kunne na kwana biyu, inda suka rufe hanyar shiga filin sauka da tashin jiragen saman wanda hakan ya haifar da tangarɗar tashin jiragen saman.