• Home  
  • Yan Sanda Sun Kamo Karin Mutane 10 Da Ake Zargi Da Siyan Baburan Sata
- Babban Labari - Labarai

Yan Sanda Sun Kamo Karin Mutane 10 Da Ake Zargi Da Siyan Baburan Sata

Rundunar yan sandan jihar kano, ta samu nasarar kama karin mutrane 10 da ake zargi da siyan baburan sata bayan kama wanda ake zargi na farko da satar Baburan jama’a. Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, a ranar […]

Rundunar yan sandan jihar kano, ta samu nasarar kama karin mutrane 10 da ake zargi da siyan baburan sata bayan kama wanda ake zargi na farko da satar Baburan jama’a.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, a ranar Alhamis din nan.

Sanarwar ta ce  an samu karin baburan sata guda 7 kuma an mayar wa da mamallakansu bisa jajircewar jami’an yan sandan.

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa dakarunsa bisa jajircewar da suka nuna wajen yaki da aikata laifuka, da kuma kare rayukan al’umma da dukiyoinsu.

Mamallaka Baburan da aka ba su

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai