• Home  
  • CP Ibrahim Bakori Ya Roki Gwamnatin Kano Ta Cika Alkawarin Da Ta Yiwa Tubabbun Yan Daba.
- Babban Labari - Labarai

CP Ibrahim Bakori Ya Roki Gwamnatin Kano Ta Cika Alkawarin Da Ta Yiwa Tubabbun Yan Daba.

  Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yi kira ga gwamnatin jihar, ta cika alkwarin data daukarwa matasan da suka ajiye makamansu daga harkar Daba da sauran miyagun laifuka. CP Ibrahim Bakori, ya bayyana hakan ne, a wajen taron da tantance wadanda suka samu kansu cikin hali mara kyau, mai taken […]

 

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yi kira ga gwamnatin jihar, ta cika alkwarin data daukarwa matasan da suka ajiye makamansu daga harkar Daba da sauran miyagun laifuka.

CP Ibrahim Bakori, ya bayyana hakan ne, a wajen taron da tantance wadanda suka samu kansu cikin hali mara kyau, mai taken tudun mun tsira, don samar da zaman lafiya ta hanyar yin amfani da dabaru  ba da karfi ba, wanda gwamnatin jihar Kano ta samar ta kaddamar tare taimakon hukumomin tsaron jihar.

Bakori ya ce yawancin matasan suna kokarin cewa anyi irin wannan abu shekaru biyu da suka gabata amma ba a ci gab aba, inda ya roki gwamnatin ta tabbata ta aiwatar abun yadda aka tsara, inda ya ce suna fatan ba za a sanya siyasa cikin wannan shiri ba, kafin cika musu alkawarin.

Kunsan matasa 1,000 ne bisa radin kansu suka ajiye makamansu domin smar musu da sana’o’in dogaro da kai , maimakon farwa mutane makamai da su yi a baya.

Tuni huukumar Hisba ta jihar Kano ta ce za ta shirya wa tubabbun ’yan daba auren gata, a wani shiri da gwamnatin jihar ke aiwatarwa domin mayar da matasa kan turbar rayuwa ta gari.

Babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya bayyana hakan bayan da matasa sama da dubu ɗaya suka aje makamai tare da yin nadama.

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf , wanda kwamishinan yada labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya ya wakilta, ya ce wannan tantancewar da rundunar ’yan sanda ta gudanar ita ce mataki na farko.

Ya ce daga baya hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA za ta sake tantance matasan, domin tabbatar da sahihancin tuban da suka yi.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnati za ta ba tubabbun matasan jari, sannan ta koya mu su sana’o’in dogaro da kai, tare da samar musu da guraben karatu ga masu sha’awar ci gaba da karatun.

Kwamishinan ’yan sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce aikin da aka ɗora musu na tantance matasan ya nuna irin jajircewar da gwamnatin Kano ta ke da shi wajen yaki da laifuka.

Daga cikin jagororin matasan da suka yi magana akwai Kamilu da Buzu Mai Kidan Gangi, waɗanda suka gode wa gwamnati da kwamishinan yada labarai da sauran shugabannin da suka tsaya domin ganin rayuwarsu ta inganta.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai