Home » Jihar Ribas: ‘Yan Sanda Sun Tabbatar Yin Garkuwa Da ‘Yan Hidimar Kasa

Jihar Ribas: ‘Yan Sanda Sun Tabbatar Yin Garkuwa Da ‘Yan Hidimar Kasa

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
‘Yan Sanda Sun Tabbatar Yin Garkuwa Da ‘Yan Hidimar Kasa a Jihar Ribas

Rundunar ‘yansandan jihar Ribas ta tabbatar da sace wasu ‘yan hidimar kasa (NYSC) wadanda har yanzu ba a tantance adadinsu ba akan titin Gabashi zuwa Yammaci (East-West) da ke jihar Ribas.

Sace Matasan NYSC din na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan da shugaban karamar hukumar Emohua ta jihar, Dakta Chidi Lloyd, ya ayyana neman wani matashi mai suna Onuigwe Wodi mai shekaru 22 ruwa a jallo har da ladan Naira miliyan 1 kan duk wanda ya bayyana in da yake, bisa samunsa da hannu wajen kashe ‘yansanda, mu’amala da kungiyar asiri, garkuwa da mutane da fashi da makami a hanyar Gabashi zuwa Yammaci da ke jihar.

Lloyd ya kuma sanar da dakatar da biyan albashin jami’an ‘yan banga ta EMOVIS sakamakon gazawar da suka yi wajen dakile karuwar miyagun laifuka a karamar hukumar.

An tare Matasan ne yayin da suke komawa Fatakwal daga sansanin masu yi wa kasa hidima (NYSC) da ke jihar Ondo, yayin da wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da motar bas din su a yankin Emohua dake kan titin Gabashi zuwa Yammaci a daren ranar Talata.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yansanda (PPRO) a jihar, Grace Iringe-Koko, ta shaida wa manema labarai a Fatakwal cewa wasu daga cikin ‘yan hidimar kasar sun kubuta daga hannun ‘yan ta’addan.

Iringe-Koko ta bayyana cewa, an tura kwararru zuwa yankin domin tabbatar da ganin an kubutar da ‘yan hidimar kasar da aka sace.

Sai dai ba ta bayyana adadin wadanda suka tsira ba da kuma adadin wadanda aka yi garkuwa da su.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?