Hukumar kula da jami’o’in ƙasar nan (NUC) ta tona asirin wasu jami’oi 49 na kasar masu ba da takardar shaidar kammala Digiri na farko ba bisa ƙa’ida ba.
Waɗannan jami’oi 49 dai ba su da lasisi da gwamnatin tarayya. Don haka, hukumar na jan hankulan al’umma musamman iyaye da masu neman digiri na farko cewa, an rufe makarantun, sabida karya dokar harkar ilimi mai lamba CAPE3 ta Tarayyar Nijeriya (2004).
Matakin da NUC ta dauka kan wadannan haramtattun jami’o’i ya nuna aniyarta na tabbatar da ingancin tsarin ilimin Nijeriya.
Hukumar ta shawarci al’umma da su tabbatar da matsayin kowace jami’a tare da NUC kafin su fara karatu acikinta, ta yadda za su kiyaye kokarinsu na neman ilimi da makomarshi.