Yan sanda sun tsare rijistaran kotu da zargin sanya kudin marayu miliyan 35 a Crypto

Ma’aikatar shari’a ta jihar Kano ta tabbatar da kama wani rijistaran kudi na babbar kotun shari’ar musulinci dake zamanta, a Goron Dutse, mai suna Mahmud Sadik, bisa zargin karkatar da kudin marayu naira miliyan talatin da biyar.

Babban magatakardar kotunan shari’ar musulinci na jihar Kano, Dr. Abubakar Haruna Khalil, ne ya tabbatar da cafke jami’in kotun sakamakon ƙorafin da magadan suka shigar akansa.

A cewarsa lokacin da suka fara yiwa wanda ake zargin tambayoyi ya tabbatar da cewa kuɗin babu su yanzu haka, wanda hakan ne ya sanya ma’aikatar shari’ar bayar da umarnin tsare a wajen jami’an yan sanda don faɗaɗa bincike akansa.

Dr. Abubakar Haruna ya ƙara da cewa rijistaran kuɗin shi ne wanda suke zargin ya ci kuɗin, amma binciken yan sanda ne kaɗai zai binciko sauran waɗanda ake zargi matuƙar da sa hannunsu.

Ya kuma tabbatar da cewa zuwa yanzu ba a sanya kuɗin a cikin asusun ma’aikatar shari’a ba, jami’in kotun ne ya yi gaban kansa ta hanyar sanya kuɗin cikin asusun sa na banki.

Babban magatakardar kotunan, ya ƙara haƙurƙurtar da magadan cewa su kwantar da hankalin za a fito mu su da ƙudinsu duk inda ya shiga, domin kotu gidan adalci ne.

 

Ana zargin jami’in kotun ya sanya kuɗin cikin harkar Crypto don samun riba mai yawa.

Daya daga cikin magadan mai suna, Abba Inuwa, ya bayyana cewa mahaifinsu ya rasu ya bar mu su wata rumfa a kasuwa, inda aka cimma matsayar siyar da ita kan kuɗi naira miliyan 35, kuma sunje kotun domin a raba musu gadon, har alƙalin kotun ya bayar da umarnin a sanya kuɗin cikin asusun ma’aikatar shari’a , amma ake zargin jami’in kotun ya sanya a cikin asusunsa na banki.

Yaka ƙara da cewa a lokuta da dabam-daban idan sunje kotun don jin yadda za a raba mu su gadon sai suka daina ganin rijistaran kuma duk lokacin da ya gansu a kotun nan danan yake barin wurin su ta nemansa su rasa, inda suka shigar da ƙorafinsa a ma’aikatar shari’ar kan kudinsu na gado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *