Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya zargi ƴan siyasan Najeriya da yin zagon ƙasa ga ci gaban ƙasar ta hanyar ɗaukar mukaman gwamnati a matsayin gadon gidansu a maimakon amanar jama’a.Da yake jawabi a ranar Laraba a yayin taro karo na 15 mai taken, “ya Isa haka” da ya gudana a jihar Legas, Sanusi II ya ce manyan ƴan siyasa a faɗin Najeriya, suna ci gaba da yin zagon ƙasa ga ci gaban ƙasa saboda suna fifita kansu, iyalansu da abokan huldarsu fiye da ƙasar.Sunusi ya ce, ‘yan siyasa suna ganin mukaman gwamnati na su ne su ta yin harkokinsu, babu ruwansu da ‘yan kasar. wanda yin hakan ba daidai bane kuma tsantsar rashin kishi ne.Sarki Sanusi na II, ya yi kira ga matasan Najeriya da su yi watsi da tsarin da ‘yan siyasa marasa kishin ƙasa suka kafa na amfani da “kabilanci, rikice-rikicen addini, da kuma son kai,” a maimakon haka, su haɗa kai don gina ƙasa.A ƙarshe, ya jaddada cewa, ikon ƙasa yana hannun ‘yan kasa ne, ba ‘yan siyasa ba, ya ƙara da cewa, kowane mutum yana da rawar da zai taka a haƙƙinsa don tallafawa ci gaban Najeriya.
2025-12-13
