Ƙungiyar ’yan ta’adda ta Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), masu alaƙa da Al-Qaida, a yankin Sahel, sun kashe Shugaban Ƙaramar Hukumar Torodi, Kyaftin Chaïbou Mali, a wani mummunan hari da suka kai a Jamhuriyar Nijar.
‘Yan ta’addar sun je gidan Kyaftin Chaïbou Mali da ƙarfe biyu na daren Litinin 5 ga watan Janairu, 2025, inda zuwa yanzu sojojin Nijar sun tabbatar da mutuwar mutane takwas.
- Rundunar yan sandan jihar Kano ta lashi Takobin hana masu yunkurin aikata laifuka sakat.
- An karya dokar ƙasa da ƙasa a Venezuela – MDD
Cikin waɗanda harin ya rutsa da su akwai Kyaftin Chaïbou Mali, matarsa mai tsohon cikin wata takwas, ‘ya’yansu huɗu, da kuma baƙi biyu da suka zo ziyara.
Ƙaramar Hukumar Torodi tana yankin Tillabéri, kimanin kilomita 60 kudu maso yammacin Niamey, babban birnin Nijar, kuma tana iyaka da ƙasar Burkina Faso, wadda ita ma ke fama da hare-haren ƙungiyar JNIM a yankin Sahel.

