Home » ‘Yan tada-ƙayar-baya da dama sun miƙa wuya Ga rundunar sojin Najeriya

‘Yan tada-ƙayar-baya da dama sun miƙa wuya Ga rundunar sojin Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya

by Anas Dansalma
0 comment dakika 20 read

Shalkwatar tsaron kasar nan ta ce ‘yan ta-da-ƙayar-baya 1,332 ciki har da iyalansu ne suka miƙa wuya ga dakarun Operation Haɗin kai a faɗin yankin arewa maso gabas cikin mako biyu da ya wuce.

Daraktan harkokin yaɗa labaran tsaro Manjo Janar Musa Danmadami ne ya ce ‘yan ta-da-ƙayar-bayan da suka miƙa wuya sun ƙunshi magidanta 222 da mata 411 sai ƙananan yara 699.

Hedikwatar tsaron ta ce tana ci gaba da tantance ɗaruruwan ‘yan ta-da-ƙayar-bayan da suka miƙa  wuya a tsawon mako biyun da ya wuce, kafin ɗaukar mataki na gaba a kansu .

Daraktan yaɗa labaran tsaron ya kuma ce dakarun sojin Nijeriya sun kashe waɗanda ya kira ‘yan ta’adda guda 8, sun kuma kama mutanen da ake zargi masu kai musu kayan buƙatun rayuwa ne 35 a daidai lokacin da suka kuɓutar da fararen hula 19.

A yayin taronta na manema labarai duk mako biyu, Shalkwatar Tsaron Najeriya a jiya Alhamis ta kuma ce dakarun ƙasar sun karɓo makamai daga ‘yan ta-da-ƙayar-baya ciki har da bindigogin AK47 guda 14 da harsasan AK47 da bindigar toka 2 da ƙaramar mashinga ɗaya da ɗaruruwan albarusan bindigogin mashinga da gurneti 36.

Janar Ɗanmadami ya ƙara da cewa manufar taƙaita kashe takardun kuɗi ta Babban Bankin Nijeriya da ƙoƙarin da sojoji ke ci gaba da yi sun taimaka wajen rage satar mutane don neman kuɗin fansa.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?