• Home  
  • Yan sanda sun buƙaci haɗin kan al’umma wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun kwayoyi a Kano
- Labarai

Yan sanda sun buƙaci haɗin kan al’umma wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun kwayoyi a Kano

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya buƙaci al’umma su haɗa kai da jami’an tsaro wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka a jihar. Kwamishinan, wanda mataimakinsa mai kula da Area Command ta Shahuci, ACP Ibrahim Umar Makarfi ya wakilta, ya bayyana hakan ne a wani taron wayar da kan […]

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya buƙaci al’umma su haɗa kai da jami’an tsaro wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka a jihar.

Kwamishinan, wanda mataimakinsa mai kula da Area Command ta Shahuci, ACP Ibrahim Umar Makarfi ya wakilta, ya bayyana hakan ne a wani taron wayar da kan ɗalibai kan illar daba da kwacen waya da shaye-shaye wanda ƙungiyar Society for Peace, Development and Education ta shirya tare da haɗin gwiwar Jami’ar Northwest Kano.

ACP Ibrahim Makarfi ya ce rundunar ’yan sanda na aiki tare da NDLEA wajen dakile matsalar, yana mai buƙatar haɗin kan iyaye, shugabanni da makarantu.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda shaye-shaye ke lalata zamantakewar iyalai da tarbiyyar yara.

Kwamandan NDLEA na Kano, CN Dahiru Yahaya Lawal, ya bayyana cewa wasu matasa na kwacen wayoyin jama’a ne domin sayarwa, su samu kuɗin sayen miyagun ƙwayoyi.

Ya buƙaci jama’a su guji sayen wayoyin da ba su san asalinsu ba, tare da jaddada cewa masu fama da wannan jaraba na buƙatar kulawa da gyaran hali.

Shi ma Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi na Kano, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, ya bayyana cewa sama da matasa miliyan 1.1 a jihar na fama da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa matsalar babbar barazana ce ga makomar matasa.

Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Mohammed Ida, ya ce shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na ƙara yawan satar wayoyi, inda wasu matasa ke sayar da wayoyin sata kan naira dubu 10 zuwa 20 domin sayen ƙwayoyi. Ya yi kira da a samar da cibiyoyin kula da masu shaye-shaye da koyar da matasa sana’o’i.

A nata jawabin, Shugabar Jami’ar Northwest Kano, Farfesa Amina Salihi Bayero, ta yaba wa waɗanda suka shirya taron da mahalartansa bisa haɗin kai da goyon bayan da suka bayar.

ƙungiyar Society for Peace, Development and Education , Auwal Abdullahi Yola, ya bayyana cewa, sun gano cewa matsalar jihar Kano a yanzu ita ce yadda za a dakile shigo da kayan maye da kuma raba matasa da harkar sha ko siyarwa domin samun al’umma nagari.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai