Kotun sauraron ƙararraki zaɓen gwamnan Kano a jihar Nassarawa, ta umarci hukumar zaɓen jihar da ta janye shaidar samun nasarar lashe zaɓen gwamnan da Injiniya Abdullahi Sule na jam’iyyar APC ya yi a zaɓen da aka yi na ranar 19 ga watan Maris ɗin shekarar da muke ciki.
Sannan kotun ta umarci hukumar zaɓen da ta ayyana David Ombugadu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya samu nasarar.
Wannan umarni ya fito ne daga bakin mai shari’a Ezekiel Ajayi wanda ya bayyana hakan a yau.
A yayin da yake bayyana jin daɗinsa, tsohon shugaban majalisar Dattawan ƙasar nan, Bukola Saraki, ya taya ɗan jam’iyyar tasu ta PDP murnar wannan nasara da ya samu a kotun.
Wannan hukunci na zuwa ne bayan an yi makamancinsa a nan Kano inda kotun ta ayyana Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen Kano, a maimakon gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda tuni ya tabbatar da shirinsa na ɗaukaka ƙara.