Home » Sojin Nijar Sun Zargi Faransa da Tunzura ECOWAS

Sojin Nijar Sun Zargi Faransa da Tunzura ECOWAS

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Sojin Nijar Sun Zargi Faransa da Tunzura ECOWAS

Shugaban mulkin soja na Nijar Janar Abdoulrahamane Tchiani ya bayyana cewa suna sane da cewa Faransa ce ke tunzura ECOWAS tana saka musu takunkumi.

Janar Tchiani ya fadi hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na kasar cikin harshen Hausa.

Inda ya kara da cewa babu wani amfani da kasashen Najeriya ko Senegal ko Benin ko Ivory Coast za su samu idan an saka wa Nijar takunkumi.

Shugaba Tchiani ya jaddada cewa suna sane, da gangan aka kai musu ta’addanci, kuma wadanda suka kai musu shi, ko da sun bar kasar ba za su bar manufarsu.

“Sharrin da suka shuka mana, suka ci amanar kasashenmu, Allah ba zai bar su ba, Allah zai saka mana,” in ji shugaban mulkin sojan na Nijar Janar Abdoulrahamane Tchiani.

Faransa ce ke son cimma wata manufa, ta ga zuwanmu zai katse mata tabbatar da wannan manufa,” in ji Tchiani.

Ya kuma jaddada cewa sojojin Faransa dake Nijar suna daf da barin kasar, lokaci kawai suke jira.

“Sojawa na bisa hanyar tafiya, da yardar Allah za su bar kasar Nijar, lokaci ne idan ya yi za su tafi.

Dangane da makomar dangantakar dake tsakanin gwamnatin Nijar da Faransa kuwa, Shugaba Tchiani ya bayyana cewa game da mu’amala ta al’ada, duk yadda Faransa ta ga dama haka za a yi, amma batun tattalin arziki, Nijar ke da iko da arzikinta.

Arzikin kasar Nijar na ‘yan Nijar ne, muna da iko da arzikinmu kuma iko ne na tabbas ba na fatar baki ba, in ji Janar Tchiani.

Ya bayyana cewa za su dauki duka wasu matakan da za su iya dauka domin ganin ‘yan kasar Nijar sun amfana da arzikin da suke da shi.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?