Majalisar dattawan Najeriya ta ce tana da burin yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin ƙasar, ta yadda za’a samar da dokar da za ta hukunta iyayen da suka ƙi kai ‘ya ‘yansu makaranta .
Shugaban kwamitin ilimi na majalisar dattawan, Sanata Lawan Adamu Usman ya ce majalisar na duba yiwuwar yin dokar ɗauri ta wata shida ga duk iyaye ko uba da ya gaza sanya ‘ya ‘yansu a makaranta.
Cikin wata tattaunawa da yayi da manema labarai, bayan gabatar da rahoton sa ga majalisar a jiya Laraba, Sanata Lawan ya ce ” muna so s yi dokar ɗaurin wata shida ga iyayen da suka ƙi sanya ya yansu a makaranta alhali yaran sun kai shekarun shiga makaranta.
Tun da farko shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio ya ce akwai yara fiye da miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, waɗanda ya ce idan ba a ɗauki matakin kula da su ba, za su iya zama ɓata-gari idan suka girma.
Shi ma Mataimakain Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin ya ce matsalar rashin zuwan yara makaranta, babbar damuwa ce ga ƙasar, wanda ya ce ta fi ƙamari musamman a yankin arewacin ƙasar.
Matsalar ƙin kai yara zuwa makarantu dai babbar matsala ce da ta ke damun al’umma musamman a yankunan karkara, inda anan ne matsalar tafi ƙamari.