Hukumar Raya Birnin Abuja ta bayyana cewa za ta fara kamen fasinjojin dake hawa achaba. Hukumar wadda ke karkashin jagorancin ministan Abuja, Nyesom Wike ta ce idan ta kama fasinjoji masu hawa achaba dole a bar yin sana’ar a birnin.
Har ila yau, hukumar ta lalata babura 478 da aka kama su na achaba a wuraren da aka haramta yin sana’ar. Akalla an shafe makwanni biyu ana wannan aiki inda gamayyar jami’an tsaro gaba daya ke sintiri don kama babura a cikin birnin da Lugbe da kuma Kubwa.
Daraktan hukumar dake wannan sintiri, Bello Abdulateef ya shawarci jama’a da rika takawa da kafa zuwa wuraren da ba su da nisa, don tsaron kansu da lafiyarsu.