Rahotanni daga garin Kwantagora a jihar Neja na nuna cewa wani kwalele-kwale ya nutse a cikin ruwa wanda ya yi sanadiyar rasuwar yayan fitaccen mawakin yabon Annabi SAW, Marigayi Sharif Rabi’u Usman Baba.Wani dan uwan mamatan Malam Usman Tijjani Baba, ne ya bayyana haka a cikin tattaunawarsa da gidan radiyon Freedom a jiya.
Usman ya ce hadarin ya faru ne da safiyar yau Alhamis a kan hanyarsu ta zuwa wani gari a cikin Kwantagora don halartar bikin Mauludi kamar yadda su ka saba a kowacce shekara.
Ya kara da cewa, bayan samun nasarar fitowa da mutane shida da jirgin ya nutse da su cikin ruwan, an garzaya da su asibiti in da a nan ne aka tabbatar da rasuwar mutum biyu daga cikinsu.Wadanda su ka rasun su ne Khalifa Sharif Fatuhu Rabi’u Usman Baba da dan uwansa Nafsuzzakiya Rabi’u Usaman Baba.
Kamar yadda dan uwan mamatan ya tabbatar an dauko gawarwakin zuwa Kano domin yi jana’izarsu a yau Juma’a da misalin karfe 2 na rana a masallacin Juma’a na Sheikh Isyaka Rabi’u da ke unguwar Gwauron dutse cikin birnin Kano.