Kwamishinan muhalli da kula da sauyin yanayin na Jihar Kano Dokta Dahiru Muhammad Hashim ya bayyana cewa hukumarsa za ta tabbatar an daina zubar da shara barkatai a fadin jihar
Kwamishinan ya baynnan hakan ne haka a yayin gangamin kwashe shara da aka fara ajiya Litinin 13 ga Janairu, 2025.
Kwamishinan ya bayyana cewa Har ila yau, wan nan garimin shirin ya sake dawo da masu sharar tituna wadanda aka raba su zuwa wurare daban-daban na manyan titunan birnin Kano.
Ma’aikatar kula da muhalli ta jihar Kano ta tabbatar da cewa aikin kawar da sharar zai gudana ne ƙarƙashin wani shirin haɗin gwiwa na kar-ta-kwana wanda zai tabbatar da cewa tulin sharar da ake fama ta shi a sassan jihar an kawar da shi cikin ƙanƙanin lokaci.
- EFCC Ta Kama Jami’an Gwamnatin Kantsina Kan Satar Miliyan Dubu 1300
- EFCC Ta Kama Jami’an Gwamnatin Katsina Kan Satar Miliyan Dubu 1300
Kwamishinan ma’aikatar, Dr Dahiru Muhammad Hashim ya ce yanzu aiki an faro shi daga kasuwanni zuwa cikin unguwanni.
Bu-gu-da-kari Dr Dahiru Muhammad Hashim ya ce za su gayyato kamfanoni su zuba jari a harkar sarrafa shara, ta yadda jama’a za su daina kallon ta a matsayin shara, maimakon haka su kalleta a matsayin wani abu da za a iya samun arziki a cikinsa.
Yayi bayanin cewa Gwamnatin jihar Kano ba zata lamunci zubar da shara a ko’ina ba, hakan tasa muka dawo da dokar sanya kwanduna a motocin haya domin kawar da duk wani datti a kan tutuna.