Daga Auwal Hussain Dukawuya
Cibiyar masana hulda da jama’a ta Najeriya (NIPR) ta yi taron karrama gwamannan jihar Jigawa Malam Umar A. Namadi da lambar yabo mafi girma ta cibiyar (DIAMOND PRIZE) bisa zamowarsa gwarzon gwamna a fannin habbaka aikin noma da samar da abinci.
Taron karramawar ya gudana ne a dakin taro na Ahmadu Bello dake babbar sakatariyar gwamnati jihar dake Dutse.
- EFCC Ta Kama Jami’an Gwamnatin Katsina Kan Satar Miliyan Dubu 1300
- An Tabbatar Da Bullar Murar Tsuntsaye A Kano
Kwamishinoni sun gabatar da makaloli kan nasarar da gwamnatin jihar ke samu, ciki har da kwamishinan yada labarai na jihar Hon. Sagir Ahmad Musa.
Taron ya samu halartar manya-manyan mutane daga ciki da wajen jihar Jigawa.